in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafuwar bankin raya kasashen BRICS na da muhimmanci
2013-03-14 15:47:47 cri
Za a bude taron koli na kasashen BRICS wato Brazil, Rasha, Indiya, China da Africa ta Kudu karo na 5 a birnin Durban, hedkwatar kasar Afirka ta Kudu daga ranar 25 zuwa 27 ga wata. An kiyasta cewa, za a tabbatar da tsarin bankin raya kasashen BRICS, wanda aka dade ana tattaunawa kansa. Masu aikin kasuwanci da cinikayya na Afirka ta Kudu suna ganin cewa, kafuwar bankin na da muhimmanci wajen kara azama kan bunkasuwar kasashen BRICS.

An labarta cewa, bankin raya kasashen BRICS zai samar da asusun hadin gwiwa domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan more rayuwar jama'a da inganta karfin muhimman hukumomin da abin ya shafa. Bankin zai kara goyon baya da kara azama kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen BRICS da sauran sabbin rukunonin tattalin arziki ta fuskar cinikayya. Bankin zai kafa wani asusu mai yawan dalar Amurka biliyan 50, wanda aka sa ran cewa, zai mara bayan wasu ayyukan more rayuwar al'umma tsakanin kasa da kasa a nahiyar Afirka.

Kwanan baya, Sandile Zungu, sakataren kwamitin harkokin kasuwanci na Afirka ta Kudu ya bayyana wa manema labaru cewa, kasashen BRICS suna gudanar da manyan ayyukan more rayuwar jama'a, amma ka'idoji da sharuddan da ake bi ta fuskar ba da rancen kudi suna kawo cikas kan saurin bunkasuwar tattalin arziki, don haka ya zama wajibi a kafa bankin raya kasashen BRICS.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China