A cikin jawabinsa, ministan kasar ya nuna yabo kan dangantakar dake tsakanin kasar Nijar da bankin BAD, kafin ya bayyana gamsuwarsa bisa kafa wannan shiri da zai kara kyautata kwarewar kasar Nijar ta fuskar cigaban tattalin arziki da zaman al'umma a kasar Nijar.
Kuma wannan a cewar minista Cisse shi ne na kara gyara yanayin harkoki, baiwa 'yan damar cin gajiyar arzikin ma'adinai da kuma shigar da bangarori daban daban wajen kula da harkokin cigaban kasa. (Maman Ada)