Cibiyar ta zabi wasu birane daga cikin kasashe 34 da ba su samun kudin shiga mai yawa ba bisa ga alkaluman da bankin duniya ya tsara, domin gudanar da wannan bincike kan biranen dake cikin wadannan kasashe 34 bisa ganin ko za su iya daga matsayansu, ko a'a cikin shekaru 10 zuwa 20 masu zuwa. Birnin Addis Ababa na kasar Habasha ya kasance na uku, bayan biranen Djakarta na kasar Indonesia da kuma Manila na kasar Philippines, yayin da babban birnin kasar Kenya, Nairobi ya cike garbin na tara cikin jerin wadannan birane.
Kana wasu birane ukun nahiyar Afirka na daga cikin birane 20 dake kan gaba da wannan binciken ya shafa, su ne, biranen Johannesburg da Cape Down na kasar Afirka ta Kudu da kuma birnin Tunis na kasar Tunisia. (Maryam)