Cibiyar nazarin tattalin arziki ta jami'ar jama'ar kasar Sin ta ba da wani rahoto a ran 16 ga watan nan dake cewa, tattalin arzikin kasar Sin na dogaro da harkokin dake bunkasuwa cikin sauri.
Misalin hakan ya hada da samar da guraben aikin yi ta hanyar raya tattalin arziki cikin sauri, don haka ba za a iya warware wannan batu ta dogaro da matakan gwamnati kawai ba, ya kamata a zurfafa yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki.
Rahoton ya ce, Sin na samun bunkasuwar tattalin arziki kusa da kashi 10 bisa dari a ko wace shekara, tsakanin sama da shekaru 30 da suka gabata a jere, tun lokacin da aka gudanar da tsarin yin kwaskwarima a gida, da bude kofa ga kasashen waje, a sa'i daya kuma ta sadaukar da abubuwa da dama. Lamarin da ya jaddada wajibcin zurfafa yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki. (Amina)