Han Jun ya bayyana hakan ne yayin taron shekara-shekara na tattaunawa kan batun nazarin zaunannun kadarorin Sinawa na shekarar 2013.
Han Jun na ganin cewa, aikin raya garuruwa zai bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, ta yadda zai iya kara bukatu, da kuma kudaden shiga ga jama'ar kasar. Amma, za a gamu da matsaloli da kalubale da dama yayin gudanar da aikin, kamar batun kwararar mutane zuwa birane daga kauyuka, wanda hakan ka iya haifar da mawuyacin hali gare su yayin zama tare da mutanen birane, kuma ba za su iya samun isasshiyar hidima ta kayan more rayuwa kamar yadda ya kamata ba, baya ga matsalar samun daidaito wajen bunkasa birane da dai sauransu. (Maryam)