Taron wanda zai gudana tsakanin ranekun 10 zuwa 12 ga watan nan ya samu halartar mataimakin shugaban asusun ba da lamuni na duniya wato IMF Zhu Min, wanda cikin jawabin da ya gabatar ya ce gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci matuka kan yaki da cin hanci da rashawa, kuma ta wannan hanya an tabbatar da samun cikakkiyar nasara kan ayyukan da aka sanya gaba, matakin da zai taimakawa kwarai wajen samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata.
Zhu Min wanda ya yi wannan tsokaci a zaman tattauna game da halin da ake ciki don gane da tattalin arzikin duniya a wannan dandali, ya kara da cewa yayin da ake kokarin bunkasa tattalin arziki yadda ya kamata, ya zama tilas a gabatar da bayanai a fili tare, da kyautata tsarin daidaita ayyuka, wadanda dukkansu ake bukatar gudanarwa ba tare da amincewa da cin hanci da rashawa ba, wanda wani batu ne da ya kasance kalubale ga dukkanin kasashen duniya a yanzu. (Zainab)