in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na kan muhimmin matsayi wajen bunkasuwar tattalin arzikin kasa da kasa, in ji IMF
2014-04-03 14:59:03 cri
Babbar shugabar asusun ba da lamuni na IMF Christine Lagarde ta yi kira ga kasa da kasa da su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu domin cimma bunkasuwar tattalin arzikin duniya cikin daidaici, ta ce, a halin yanzu, kasar Sin na kan muhimmin matsayi wajen bunkasuwar tattalin arzikin kasa da kasa.

Christine Lagarde ta bayyana haka ne yayin da take ba da jawabi a babbar kwalejin nazarin harkokin kasa da kasa ta jami'ar Johns Hopkins dake kasar Amurka a ranar 2 ga wata.

Ta kuma kara da cewa, ministocin harkokin kudi da shugabannin manyan bankuna na G20 sun cimma matsayi daya a yayin taron Sydney da aka gudana a watan Fabrairun da ya gabata cewa, idan kasa da kasa za su iya daukar manufofin kudi da za su dace, tare da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, to za a iya daga kashi biyu bisa dari na GDP na kasa da kasa cikin shekaru biyar masu zuwa.

A sa'i daya kuma, madam Christine Lagarde ta ambaci wasu matakan gyare-gyaren da asusun IMF ya zartas a karshen shekarar 2010, inda ya tsai da kudurin samar da kashi 6 bisa dari na asusun ga kasashen dake samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri da kuma kasashe masu tasowa wadanda ba su samun bunkasuwa yadda ya kamata ba, don gane dagawar matsayin wadannan kasashe cikin bunkasuwar tattalin arzikin kasa da kasa, za a kira jefa kuri'u kan zaben shugabannin gudanarwar na IMF, ta yadda za su iya wakiltar moriyar bangarorin da abin ya shafa yadda ya kamata.

Cikin jawabinta, Lagarde ta kuma bayyana cewa, kusan dukkan mambobin kasashe na IMF sun cimma matsayi guda kan daftarin gyare-gyaren nan, amma, ban da kasar Amurka wadda ke daukar hanayen jari mafi yawa na asusun IMF, shi ya sa, har zuwa yanzu, IMF bai iya gudanar da daftarin ba.

IMF zai gabatar da sabon hasashen da ya yi game da yanayin tattalin arzikin kasa da kasa cikin mako mai zuwa.

Madam Lagarde na ganin cewa, saurin karuwar tattalin arziki na wasu kasashe masu samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri a nahiyar Asiya zai kasance gaba cikin kasa da kasa a shekarar da muke ciki, kuma kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China