Hua Chunying ta bayyana haka ne a yayin taron maneman labarai da aka saba yi a nan birnin Beijing, inda ta kuma yi bayani game da ziyarar da tawagar wakilan kasar Sudan ta Kudu suka kawo nan kasar Sin.
Bisa gayyatar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi masa, shugaban kwamitin harkokin wajen kungiyar adawa ta kasar Sudan ta Kudu Dhieu Mathok Diing Wol ya kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin tare da wata tawagar kasar.
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da mataimakinsa Zhang Ming sun gana da tawagar Sudan ta Kudu a jiya Litinin 22 ga wata, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a iya warware matsalar kasar Sudan ta Kudu ta hanyar zaman lafiya.
Hua Chunying ta kara da cewa, kasar Sin tana maraba da kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka ta IGAD da ta taimaka wa kasar Sudan ta Kudu wajen warware matsalar kasar, don kiyaye zaman lafiya da zaman karko na kasar Sudan ta Kudu da na yankin baki daya, haka kuma, tana son taimakawa kasar wajen hanzarta warware matsalar dake fuskanta daga dukkan fannoni yadda ya kamta. (Maryam)