in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD ta bayyana alhininta game da kisan jami'i mai shiga tsakani a Sudan ta Kudu
2014-08-25 10:23:17 cri

Kungiyar bunkasa yankin gabashin nahiyar Afirka ta IGAD, ta yi Allah wadai da kisan daya daga jami'anta masu aikin shiga tsakani a rikicin kasar Sudan ta Kudu.

Wata sanarwa da kungiyar ta IGAD ta fitar ta dora alhakin kisan wannan jami'i da aka hallaka a garin Bentiu, kan mayakan 'yan tawayen Sudan ta Kudun, masu biyayya ga korarren mataimakin shugaban kasar Riek Machar.

Da yake yiwa manema labaru karin haske game da wannan batu, jagoran ma'aikata masu aikin shiga tsakani na kungiyar ta IGAD Seyoum Mesfin, ya ce, wadanda suka karya yarjejeniyar tsagaita wuta, da masu hannu cikin kisan wancan jami'i, za su fuskanci hukuncin ta'asar da suka aikata.

Mesfin wanda ke wannan tsokaci a jiya Lahadi, gabanin bude wani taron bazata na shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta IGAD a birnin Addis Ababan kasar Habasha, ya kara da cewa, za a yi amfani da damar taron wajen lalubo mataki na gaba da ya dace a dauka, tare da bayyana hukuncin dake da nasaba da hakan, kamar yadda yake kunshe cikin sanarar bayan taron kungiyar, na ranar 10 ga watan Yunin da ya gabata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China