Zaman taro karo na shida na zagayen shawarwari na biyu kan zaman lafiya a Sudan ta Kudu ya bude a ranar Litinin a Bahir Dar, wani birnin kasar Habasha dake arewa maso yammacin kasar, in ji hukumar kasa da kasa kan cigaba ta IGAD, wata gamayyar shiyyar gabashin Afrika a cikin wata sanarwa.
Gyare-gyaren mulkin rikon kwarya, matakan kafa kundin tsarin mulki na din din din, gyare-gyaren da suka shafi tsaro cikin mulkin wucin gadi, kulawa da albarkatun tattalin arziki da na kudi, kana da batun shari'a da sasantawa game da rikon kwarya suna cikin manyan batutuwan da mahalarta taron za su mai da hankali kan su, in ji sanarwar. (Maman Ada)