Kakakin MDD Stephane Dujarric ya ce, binciken da tawagar UNMISS dake Sudan ta Kudu ta gudanar ya nuna cewa, wasu ne suka harbo jirgi mai saukar ungulu na MDD mai lamba Mi-8 ran 26 ga watan da ya shude, lamarin da ya haddasa kisan jami'ai uku dake cikin sa 'yan kasar Rasha, tare da raunata karin wasu mutanen 4.
Dujarric wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a jiya Talata, ya kara da cewa, binciken kwararru ya nuna jirgin wanda aka kakkabo, na hanyarsa ne daga garin Wau dake yammacin jihar Bahr El-Ghazal zuwa Bentiu, ya kuma fadi a wani wuri mai nisan kilomita 10 daga kudancin birnin Bentiun jihar Unity.
Kaza lika kakakin na MDD ya tabbatar da cewa, yayin wata tattaunawa da wani jami'in tawagar UNMISS mai suna Peter Gadet ya yi da kwamandan 'yan adawar kasar a jihar Unity ranar 17 ga watan Agusta, kwamandan ya yi zargin ana amfani da wani jirgi domin daukon makamai ga dakarun gwamnatin kasar, don haka ya yi barazanar kakkabo wannan jirgi. (Saminu)