Ministan ma'aikatar wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana daukar matakan siyasa a matsayin hanyoyin da suka fi dacewa, wajen warware rikicin dake ci gaba da addabar kasar Sudan ta Kudu.
Mr. Wang wanda ya bayyana hakan ga takwaransa na Sudan ta Kudu Marial Benjamin a nan birnin Beijing, ya kara da cewa, dakatar da bude wuta tsakanin sassan da ba sa ga maciji da juna a Sudan ta Kudun, babban sharadi ne na kaiwa ga warware rikicin kasar.
Kaza lika Wang ya ce, kamata ya yi kasashen Afrika, su warware matsalolin da ke addabar su da kan su, bisa kuma wannan manufa ne kasar Sin ke goyon bayan gudummawar da kungiyar IGAD ke bayarwa a wannan fanni.
Daga nan sai ya bayyana aniyar kasar sa, ta ci gaba da baiwa Sudan ta Kudu dukkanin tallafin da ya wajaba kamar dai yadda ta saba.
A nasa bangare Mr. Benjamin cewa ya yi, kasar sa na martaba alakar dake tsakanin ta da Sin, tare da jinjinawa kokarin da Sin din ke yi na kawo karshen rigingimun dake addabar Sudan ta Kudu.
Ya ce, a halin da ake ciki, daukacin masu ruwa da tsaki, na matsa kaimi wajen ganin an kai ga cimma burin dakatar da musayar wuta, tare da warware matsalolin dake addabar kasar ta hanyar lumana. (Saminu)