in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada Ellen Loj a matsayin wakiliyar musamman ta MDD a Sudan ta Kudu
2014-07-24 10:48:28 cri

Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya sanar a ranar Laraba da nada madam Ellen Margrethe Loj, 'yar kasar Danmark a matsayin sabuwar wakaliyar musamman, kana kuma shugabar tawagar MDD a Sudan ta Kudu (MINUSS). Madam Loj ta maye gurbin 'yar kasar Norway madam Hilde Johnson da ta zo karshen aikinta a ranar 7 ga watan Julin shekarar 2014. Sakatare janar na MDD ya nuna godiyarsa ga madam Johnson bisa juriyarta wajen aikin da ta gudanar a matsayin shugabar MINUSS tun kafuwar wannan tawaga a cikin watan Julin shekarar 2011, in ji kakakin Ban, mista Farhan Haq a cikin wata sanarwa.

Madam Loj mai shekaru 65 da haifuwa, za ta ba da babban taimako kan wannan matsayi bisa ga kwarewarta game da ayyukan wanzar da zaman lafiya da na harkokin kasa da kasa, bayan ta rike mukamin wakiliyar musamman ta sakatare janar a cikin tawagar MDD dake kasar Liberiya daga shekarar 2008 zuwa shekarar 2012, in ji kakakin Ban Ki-moon.

Sudan ta Kudu tana fama da tashe-tashen hankali tun daga watan Disamban shekarar 2013, bayan raba gari tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar da aka zarge shi da yunkurin juyin mulki. Rikicin kasar ya yi sanadiyyar mutuwar miliyoyin mutane, kana mutane miliyan 1,5 suka kaura daga gidajensu, a yayin da mutane fiye da miliyan bakwai suke fuskantar bazaranar yunwa da cututtuka. Kwamitin tsaro na MDD ya kara tsawon wa'adin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Sudan ta Kudu har zuwa ranar 30 ga watan Nuwamban wannan shekarar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China