in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta karbi maganin cutar Ebola daga Japan
2014-09-02 10:46:29 cri

Ministan lafiya na Najeriya Onyebuchi chukwu ya bayyana cewa, nan ba da dade wa ba Najeriya za ta karbi wani maganin cutar Ebola mai suna Favipiravir daga kasar Japan.

Ministan wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, a Abuja, fadar mulkin kasar ya kuma ce, baya ga wannan magani da zai shigo kasar daga Japan, akwai kuma wani maganin yaki da cutar da kuma wasu magunguna guda biyu da wata kungiyar binciken magunguna da ke Najeriya mai suna TRG ta gano.

Ya ce, kungiyar ta TRG tana kokarin gano wani maganin gwaji mai kama da Zmapp, ta kuma baiwa gwamnati shawarwari don gudanar da bincike kan wadannan magunguna da kuma wasu magungunan rigakafi da warkar da cutar.

Ministan ya ce, an yi la'akari da wannan magani ne saboda imanin da aka yi cewa, yana da sinadaran yaki da cutar ta Ebola, sannan ba shi da illa bayan da ya cika dukkan sharuddan gwaje-gwajen likitoci na kasancewa maganin da za a yi amfani da shi a yanayi na gaggawa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China