in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen gabashin Afrika na fatan hada karfinsu domin yaki da cutar Ebola
2014-08-07 10:35:34 cri
Kasashen gabashin Afrika sun bayyana fatansu a ranar Laraba na karfafa dangantakarsu domin yaki da cutar Ebola dake shafar wasu kasashen yammacin Afrika.

An dauki wannan mataki a yayin taron musamman na ministocin kiwon lafiya na shiyyar kungiyar SADC da aka shirya a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.

Ministocin sun cimma wasu matakan da za su taimaka wajen fuskantar duk wata bullowar cutar Ebola, ko da yake har yanzu ba'a gano Ebola har zuwa yanzu a gabashin Afrika.

Ministan kiwon lafiya na kasar Malawi, Jean Kalilani, kuma shugaban taron ministocin kiwon lafiya na kungiyar SADC ya shaida wa manema labarai cewa jami'an sun yi kira ga kasashe mambobi da su gaggauta hanyoyin dakile wuraren Ebola a shiyyar.

Fadakar da jama'a kan Ebola zai taimakawa al'ummomi maida martani yadda ya kamata kan wannan annoba, in ji mista Kalilani.

Mun amince shirya tuntubar juna kan iyakoki domin kawo sauki ga musanyar bayanai da kula da dangantakar hadin gwiwa domin karfafa wajen sanya ido, bincike, isar da sako, da sauransu da ma musanyar bayanai tare da hukumomin da abin ya shafa da kuma kungiyar kiwon lafiya ta duniya (OMS), in ji shugaban wannan taron.

Ministocin kiwon lafiya sun amince wajen kara kafa cibiyoyin kiwon lafiya da za'a amfani da su da zaran an samu bullowar cutar Ebola da kuma samar da kayayyaki ga wadannan cibiyoyin bisa umurnin OMS. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China