An gano wasu mutanen dake dauke da cutar Ebola a gundumar Equateur dake arewa maso yammacin DRC-Congo, a cewar wata majiyar ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar da ba'a ambato sunanta ba a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Laraba. A cewar wannan majiya, kusan mutane takwas ne ake zaton suna dauke da wannan cuta a gundumar. Ministan sadarwa na kasar kuma kakakin gwamnati, Lambert Mende ya karyata wannan labari a lokacin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya tuntube sa ta wayar tarho. (Maman Ada)