in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO za ta kira taro kan cutar Ebola
2014-08-06 10:45:50 cri

Kwamitin lura da ayyukan gaggawa na hukumar lafiya ta duniya WHO, zai gudanar da wani taro na yini biyu, domin tattauna batutuwan da suka shafi barkewar cutar nan ta Ebola a yankunan yammacin Afirka, da kuma tantance ko annobar ta kai ga matsayi na kasancewa barazana ga daukacin sassan duniya baki daya.

Hakan a cewar mataimakiyar mai magana da yawun MDD Vannina Maestracci, ya biyo bayan kididdigar da WHO ta fitar, wadda ke nuna cewa, ya zuwa ranar 1 ga watan Agustan nan, adadin mutanen da suka kamu da cutar ya kai 1,603, ciki had da mutane 887 da tuni suka rasa rayukansu.

An dai samu bullar cutar ta Ebola ne a kasashe 4 dake yammacin Afirka, da suka hada da Guinea, da Liberia, da Najeriya da kuma kasar Saliyo.

Tuni kuma a cewar Vannina Maestracci aka fara tattara tallafin kudade, da na kwararru daga hukumomin dake hadin gwiwa da WHO, da na MDD, tare da ma sauran masu ruwa da tsaki.

A kuma ranar Jumma'a mai zuwa ne ake sa ran gudanar da wani taron manema labaru, tare da mataimakin babban daraktan tsaron lafiya na WHO Dr. Keiji Fukuda a birnin Geneva, domin fayyace sakamakon taron kwamitin gaggawar hukumar wanda zai fara zamansa a Larabar nan. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China