Ministan lafiya na Nigeriya Onyeabuchi Chukwu, ya ce, Nigeriya ta samu nasarar dakilar da yaduwar cutar Ebola mai saurin kisan jama'a.
Ministan lafiyar wanda ke jawabi, jim kadan bayan taron mako-mako na majalisar gudanar da mulki ta tarayyar Nigeriya a Abuja, babban birnin kasar, ya shaida wa manema labarai sabbin bayanai game da bullar cutar ta Ebola a Nigeriya.
Ministan ya bayyana cewa, a halin da ake ciki, mutane 2 ne kacal ke fama da cutar a Nigeriya, kuma ya bayyana cewar, gwamnatin Nigeriya na samun sakonni yabo daga kungiyoyi na duniya da kuma gwamnatin Amurka, a game da yadda Nigeriya ta dauki matakai na hana yaduwar cutar ta Ebola a Nigeriya.
Chukwu ya ce, gwamnatin Nigeriyar na duba yiwuwar karrama dukanin wadanda cutar ta Ebola ta hallaka, musamman jami'an lafiya wadanda suka rasa rayukan su a sakamakon cutar ta Ebola.
Chukwu ya ce, gwamnatin kasar na ci gaba da yin alaka da iyalan likitar nan ta Nigeriya, da ta rasu a sakamakon cutar ta Ebola.
Ministan lafiyar na Nigeriyar ya ce, gwamnatocin yammacin Afrika suna sa ido a kan mutane kimanin 177 masu jiyyar cutar Ebola. (Suwaiba)