A kwanakin baya ne, aka gano wasu mutane da aka zarge su da kamuwa da cutar ta Ebola a kasashen Jamus, Spaniya, Romania, Ruwanda, Senegal da sauran kasashe, amma aka janye zargin da ake musu daga baya. Ya zuwa yanzu, ban da kasashen Liberia, Saliyo, Guinea da Nijeriya, ba a gano wasu mutane da aka tabbatar sun kamu da cutar ta Ebola a wasu kasashe da yankuna ba.
Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta bayyana a ranar 19 ga wata cewa, ana ci gaba da samun bunkasuwa a sha'anin yawon shakatawa a kasar, inda yawan masu yawon shakatawa daga kasashen waje bai ragu ba duk da matsalar cutar Ebola a Afirka. Ministan harkokin sadarwa na kasar Afirka ta Kudu Faith Muthambi ya bayar da wata sanarwa a wannan rana cewa, babu wani mutum da ya kamu da cutar Ebola a kasar ba. Kana ya ce, Ko da za a samun wanda ya kamu da cutar a kasar a wata rana, gwamnatin kasar na da imani da karfin tinkarar matsalar, bisa kyakkyawan tsarin sanya ido kan cututtuka da isassun na'urorin bada jinya da take da su. (Zainab)