Babbar darakta a hukumar lafiya ta duniya WHO Margaret Chan, ta ce, ya zuwa yanzu babu wasu alamu dake nuna yiwuwar kawo karshen cutar nan ta Ebola cikin hanzari.
Chan wadda ta bayyana haka cikin wani sharhi da ta rubuta a wata mujallar kiwon lafiya ta kasar Amurka, ta kara da cewa, akwai bukatar kasashen duniya su daura damarar ba da karin taimako, ga yakin da ake yi da wannan cuta a kasashen yammacin Afirka, inda tuni ta hallaka sama da mutane dubu daya.
Ta ce, bullar cutar a wannan karo ta yi muni kwarai, kuma fatara da talauci na cikin manyan dalilan dake kawo cikas ga yakin da ake yi da yaduwar ta.
A sharhin nata, Chan ta zayyana kasashen Guinea, da Liberia, da Saliyo, inda cutar ta fi tsananta da kasashe mafiya fama da talauci, wadanda kuma ba su dade da fita daga yake-yake ba, kana suna da rauni wajen harkokin da suka shafi kiwon lafiya.
Kari kan hakan, jami'ar ta WHO ta ce, batun rashin ayyukan yi, da gujewa asibitoci, ko cibiyoyin kula da masu dauke da cutar da wasu mutane ke yi, tare da mu'amala da gawawwakin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da ita, na cikin karin kalubale da ake fuskanta. Baya ga amincewar da wasu ke yi da batun amfani da wasu hanyoyin gargaji na magani ko riga kafin cutar ta Ebola. (Saminu)