in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a hada kai wajen yin kwaskwarima yadda ya kamata, in ji shugaban kasar Sin
2014-08-18 20:56:01 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taro karo na hudu na rukunin mai jagoranta aikin zurfafa kwaskwarima a dukkan fannoni a kasar Sin a safiyar yau Litinin 18 ga wata. A cikin jawabin da ya gabatar wajen taron ya ce, ya kamata kamfanonin dake karkashin gwamnatin kasar musamman ma wadanda ke karkashin kwamitin tsakiya, su mallaki wasu muhimman sana'o'i dake da nasaba da tsaron kasar da tattalin arzikin al'ummar kasar. A ganin sa wadannan kamfanoni sune suka kasance ginshikin tattalin arzikin kasar Sin, abinda yasa suka zama babban madaurin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da mulkin gurguzu mai tsarin musamman na Sin, don haka bunkasa su yadda ya kamata yana da muhimmanci (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China