Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bukaci da a samar da manyan canje-canje tare da daidaita tsarin masana'antu, domin ci gaba da dorewar habbakar tattalin arziki a matakin da ya dace.
Li, ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba, a yayin da ya jagoranci wani taron bita a kan tattalin arzikin kasa a wadansu larduna. Taron bitar wanda aka yi a lardin Liaoning, ya samu halarcin manyan jami'an daga lardunan Liaoning, Zhejiang,Anhui da Guangdong da kuma birnin Chongqing wanda gwamnatin Sin ke mulkin sa kai tsaye.
Li, ya kara da cewar, kwaskwarima wani abu ne dake zaburar da ci gaba, tare da kara kaimin fasahar miliyoyin jama'a.
Firaministan ya ba da umurni cewar, hukumomin da abin ya shafa, a majalisar zartaswar kasa su samar da sauye-sauye na ayyukan gwamnati, abin da kuma ya bukaci lardunan da su gudanar da nazari tare da duba sigar matsalolin da ake samu, ta yadda za'a sami sassaucin tafiyar da kasuwanci.
Li, ya kara da cewar, ana bukatar girka habbakar tattalin arzikin akan matakin da ya dace, a inda ya yi nuni da cewa, tattalin arzikin kasar Sin, ya nuna alamun samun canji na cigaba a farkon wannan shekarar.
To amma firaministan ya ce, bai kamata a kauce sa ido akan matsaloli da kalubale da tattalin arzikin ke samu ba. (Suwaiba)