in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron JKS da za'a yi a Nuwamba zai tattauna kan karfafa matakan kwaskwarima
2013-08-28 15:11:02 cri

Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS zai kira wani taro a watan Nuwamba mai zuwa domin tattauna matakan karfafa kwaskwarima ta ko wane fanni, kamar yadda ofishin kwamitin kula da al'amuran siyasa ta jam'iyyar ta sanar a ranar Talatan nan.

Ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS mai mambobi 25 a cikin wata sanarwar ya ce, za a yi cikakken taro na uku na babban taron karo na 18 a birnin Beijing, babban birnin kasar a watan Nuwamban bana.

Taron wanda babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Xi Jinping ya jagoranci zaman ya amince da tsarin ayyuka tsakanin shekarar 2013 da ta 2017 da aka gabatar na kafa tare da inganta dokar hukunci da hana aiwatar da cin hanci da rashawa.

Sanarwar ta kara da cewa, har ila yau, taron ya amince da wata takarda da ta shafi ayyukan kwaskwarima kan hukumomi na kananan gwamnatocin jihohin kasar.

A lokacin wannan zama, mambobin ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS sun saurari rahoton da aka shirya na ayyukan da aka yi a shiyyar kasuwanci maras shinge a birnin Shanghai. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China