Sharhin ya bayyana cewa, ba kawai harkokin hadin gwiwar da kasar Sin ta yi tare da kasashen Afirka suka tallafawa kasar Sin ba, har ma sun baiwa kasashen Afirka kayayyakin more rayuwa da suke bukata, da kuma tallafin kudi. Kana, a halin yanzu, kasar Sin ta kasance babbar abokiyar ciniki ta kasashen Afirka, ita ma abokiyar siyasa ta nahiyar Afirka, kwanan baya, kasar Sin ta kuma ba da muhimmin taimako ga yammacin kasashen Afirka wajen yaki da cutar Ebola.
Hakan ya sa, shugabannin kasashen Afirka suna mai da kasar Sin a matsayin abokiyarsu, a maimakon irin kasashen dake neman nuna karfin siyasa da nuna iko kan wasu kasashe da dama. Bugu da kari, sharhin ya bayyana cewa, ba shakka kasar Sin na ba da taimako ga bunkasuwar kasashen Afirka, da kuma daukaka matsayansu cikin harkokin kasa da kasa. (Maryam)