in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bikin tattaunawa kan hadin kai da zuba jari ga kasashen waje karo na biyar a nan birnin Beijing
2013-12-03 16:27:59 cri

An gudanar da bikin tattauna kan hadin kai da zuba jari ga kasashen waje, karo na biyar daga ran 3 zuwa 4 ga watan nan a dakin baje koli dake nan birnin Beijing.

Taron na wannan karo ya samu halaratar kamfanoni, da hukumomin hada-hadar kudi, da na bincike na gida da na waje kimanin 2200, baya ga hukumomi fiye da 160 daga kasashe ko yankuna 50, da suka kafa runfunan su.

Wannan taro ya kuma samar da wata dama mai kyau ga kamfanonin cikin gida da ma na ketare, kan batun bunkasa zuba jari. Har ila yau ya ba da damar gabatar da bukukuwa da dama, da suka shafi wasu manyan batutuwa masu alaka da dangantakar bangarori daban-daban, ciki hadda dandalin kamfanonin Sinawa masu zuba jari a nahiyar Afrika, da dandalin kamfanonin Sinawa masu zuba jari a nahiyar Latin Amurka, da ragowar sassa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China