in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta daidaita dokoki game da zuba jari a cikin gida da waje
2013-11-19 16:35:29 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin Shen Danyang ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Talata 19 ga wata cewa, za a sa kaimi kan daidaita dokoki game da zuba jari a cikin gida da waje, da tabbatar da aiwatar da manufofin yin amfani da jarin waje yadda ya kamata, da kuma kafa tsarin zuba jari cikin adalci.

Shen Danyang ya bayyana cewa, za a sa kaimi ga bude kofa a fannonin hada-hadar kudi, bada ilmi, kiwon lafiya da sauransu, kana za a sassauta kayyadewar da aka yiwa shirin zuba jari da kasashen waje suka yi a fannonin samara da karfe, sarrafa sinadarai da dai sauransu.

Ban da wannan kuma, Shen Danyang ya nuna cewa, kasar Sin za ta bukaci kamfanonin kasa da kasa da su kafa cibiyoyin nazari da sayen kayayyaki a kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China