Kasar Afrika ta Kudu ta zuba a shekarar 2011 zuwa shekarar 2012 kusan kimanin kudin Rands biliyan biyu, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 190 wato fiye da na shekarar 2010 zuwa shekarar 2011 a fannin bincike da cigaba (R&D), a cewar wasu alkaluma masu tushe da aka fitar a ranar Talata.
Tare da wannan karuwa, kudin da ake kashewa a fannin bincike da cigaba (DBRD) ya kai kudin Rands biliyan 22,2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2,1, in ji ma'aikatar kimiyya da fasaha (DST) ta kasar. Haka kuma tare da wannan karuwa na jimillar adadi, kudin da aka kashe kan aikin bincike da ci gaba ya kan kashe 0,76 cikin 100 na GDP na Afrika ta Kudu, irin adadin da aka samu a shekarar 2010 zuwa shekarar 2011. (Maman Ada)