in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ce kadai ke cikin jerin kasashe 25 masu janyo jari daga ketare
2014-06-05 10:55:26 cri

Wani rahoto da cibiyar bincike kan harkokin gudanarwa ta AT Kearney ya fitar, ya nuna cewa, kasar Afirka ta Kudu ce kadai kasa daya tilo a nahiyar Afirka, dake cikin jerin kasashen duniya 25 masu cikakken ikon janyo hankulan masu zuba jari daga ketare.

Alkaluman kididdigar dake hasashen sha'awar masu juba jari a kasashe na FDI, wanda cibiyar ta AT Kearney ta yi amfani da su wajen fidda rahoton nata, sun nuna cewa, Afirka ta Kudun ta dada samun ci gaba a wannan fage, inda a yanzu ta gusa zuwa matsayi na 13 a jerin kasashen 25. Kaza lika kasar Amurka ta ci gaba da rike matsayinta na daya a wannan jadawali, yayin da kasar Sin da Canada ke biye a matsayin na biyu da na uku.

Wannan sakamako dai ya faranta ran mahukuntan kasar Afirka ta Kudu, wadanda suka bayyana hakan a matsayin manuniya dake haskaka irin ci gaba da kasar ke samu, a fagen hadin gwiwa da kasashen ketare a harkokin zuba jari.

A cewar babban jami'in ofishi mai kula da harkokin samar da bayanai na gwamnatin kasar Phumla Williams, Afirka ta Kudun na iyakacin kokari wajen baiwa masu sha'awar zuba jari daga ketare dama, ta habaka hada-hadar su, a matsayinta ta jigo a wannan fanni a Afirka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China