in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Thomas Bach ya zama sabon shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya
2013-09-11 15:04:08 cri
A ranar 10 ga watan nan da muke ciki ne, aka gudanar da zaben jagorancin kwamitin wasannin Olympics na duniya, inda a gun cikakken zaman taro karo na 125, da aka yi a birnin Buenos Aires da ke kasar Argentina, Thomas Bach, dan kasar Jamus ya samu akasarin kuri'un da aka kada yayin zabe zagaye na biyu, ya kuma zama shugaba na 9, na wannan kwamitin wasanni mafi girma a duniya, inda zai shafe tsawon wa'adin aiki na shekaru 8 wato i zuwa shekarar 2021.

Cikin jawabinsa na godiya Bach, ya yabawa tsohon shugaban kwamitin Jacques Rogge, da sauran mambobin kwamitin bisa goyon baya da suka nuna masa, yana mai alkawarin yin iyakacin kokarin aiki, da sauraron ra'ayoyi daga bangarorin daban daban, don kokarta samar da daidaito da adalci ga duk wanda ya shiga wasannin Olympics, wato dai, zai zama shugaban kwamitin na kowa.

Bisa tsarin dokar shugabancin kwamitin, sabon shugaban kwamitin na da wa'adin aiki na tsawon shekaru 8 a zangon farko, da kuma karin shekaru 4, idan har ya sake lashe zabe a karo na biyu.(Bako).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China