in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kokarta kyautata bada ilimi a kauyuka
2014-02-13 16:59:48 cri
Bisa labarin da wakilinmu ya samu a gun taron ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin a ranar 13 ga wata, an ce, kasar Sin ta yi shirin kyautata ayyukan makarantu a kauyuka cikin shekaru 3 ko 5 masu zuwa.

Domin gaggauta kyautata halin da ake ciki ta fannin bada ilimi a yankunan da ke fama da talauci, gwamnatin Sin ta tsara shirin kyautata sha'anin inganta ayyukan bada ilimi a cikin makarantun wadannan wurare, ta hanyar aiwatar da abubuwan da ke kunshe cikin wannan shiri, sassan da abin ya shafa na kasar Sin za su yi kokari cikin shekaru 3 ko 5 masu zuwa, domin biyan bukatun 'yan makaranta na samun dakunan karatu, teburori, kujeru, laburare, na'urorin bincike da filayen motsa jiki a cikin makarantun yankunan da ke fama da talauci, kana dalibai za su samu dakunan kwana, da gado da wurin ban haya, dakunan cin abinci da ruwan sha. A game da yaran da iyayensu ke cin rani a cikin birane, za a biya bukatunsu na samun ilmi da kuma wurin kwana a cikin makaranta. Har wa yau, za a inganta ayyukan koyarwa a makarantun firamare dake cikin kauyuka yadda ya kamata.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China