Ma'aunin kare ikon mallakar fasaha ta duniya na shekarar 2013 ya nuna cewa, a shekarar 2012 yawan shaidar ikon mallakar fasaha da aka nema a duniya a wannan shekara ya kai kimanin dubu 2350.
Har ila yau hukumar kare ikon mallakar fasaha ta kasar Sin ta samu rokon neman shaidar, da yawansu ya kai dubu 653 a bana kadai, wanda hakan ya nuna karuwar adadin da kashi 24 cikin 100 bisa na bara, yawan karuwar ya kai matsayi na farko a duniya baki daya.
A shekarar 2012, yawan shaidar ikon mallakar fasaha da Sinawa suka nema ya kai dubu 561, adadin da ya kai matsayi na farko a duniya. Bisa rahoton da aka bayar, an ce a cikin kasashen da ke da matsakaitan kudin shiga, kasashen Sin da India ne kawai suke cikin jerin kasashe 20 na farko, a neman shaidar ikon mallakar fasaha.(Bako)