Ofishin kula da harkokin ba da ilmi na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ya bayyana a 'yan kwanakin baya cewa, yawan kudin da aka zuba a fannin ba da ilmi a jihar Tibet ya kai kudin Sin Yuan biliyan 11 a shekara ta 2013. Yawan yaran da suka shiga cikin makarantun firamare ya kai kashi 99.59 bisa dari, yayin da yawan wadanda suka shiga makarantun sakandare ya kai kashi 98.75 bisa dari.
Darektan ofishin kula da harkokin ba da ilmi na jihar Tibet Mista Ma Shengchang ya bayyana cewa, a shekara ta 2013, an gudanar da manufofi 43 domin ba da taimako ta fuskar ba da ilmi, haka kuma an kebe kudin da yawansa ya kai Yuan biliyan 1 da miliyan 891, dalibai da malamansu da yawansu ya kai miliyan 1 da dubu 33 da dari 4 suka samu taimako daga wannan asusu. A shekara ta 2013, an kebe kudin Yuan biliyan 1 da miliyan 381 domin samar da abinci, wuraren kwana da kayan karatu ga 'yan makaranta, lamarin da ya amfanawa 'yan makaranta fiye da dubu 520, wadanda suka kai kashi 95 bisa dari na 'yan makarantar baki daya.(Danladi)