in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira da shigar da darasin koyar da da'a cikin makarantun Najeriya
2014-07-01 09:42:23 cri

Malaman makaranta a Najeriya sun kare a ranar Litinin matakin sake maido da darasin koyar da da'a a cikin makarantun faramare da sakandare domin kawo karshen tabarbarewar da'a daga wajen matasa.

Joseph Nweke, shugaban kungiyar malaman makarantar Najeriya (NUT) dake cikin jihar Ebonyi, ya yi wannan kiran a birnin Abakaliki, hedkwatar jihar dake kudu maso gabashin tarayyar Najeriya, inda ya bayyana cewa, kasar na cikin wani mawuyacin lokaci. Mista Nweke ya danganta wannan matsalar kan tabarbarewar da'a cikin sauri, tare da kara cewa, matsalar na janyo babbar barazana ga zaman jituwar al'ummar kasar baki daya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China