A shekarar 2010, kasar Sin ta gudanar da shirin kyautata makarantu ta hanyar tilastawa bada ilmi a kauyuka, da kokarin kawar da matsalolin da suke kawo tarnanakaki wajen raya sha'anin ilmi a kauyuka, haka kuma za a cigaba da kokari wajen raya kayayyakin koyarwa, da gyara makarantu.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2013, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta riga ta ba da kudaden agaji da yawansu ya kai kudin Sin RMB biliyan 65.68 domin taimakawa raya fannin ilmin kasar baki daya.(Bako)