in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gudanar da bikin baje koli kan ilmi a babban birnin Mozambique
2014-05-16 14:23:59 cri

Wakilan jami'o'i daga Zimbabwe, Brazil, Portugal, Afrika ta Kudu, Swaziland, Sweden da Angola a jiya Alhamis sun kasance a Maputo, babban birnin kasar Mozambique, inda suka shiga bikin baje koli ta duniya a kan ilmi, domin musayar fasahohi tsakanin dalibai da kuma kwararru dake halartar taron.

Shi dai wannan baje koli na ilmi, kungiyar malamai masu raya ilmi tare da hadin gwiwar ma'aikatar ilmi ta Mozambique ne suka shirya shi da zummar samar wani yanayi na tattaunawa da juna tsakanin hukumomin ilmi daban daban da suka halarci baje kolin.

A wannan shekarar, an yi murnar bikin baje kolin ne a karkashin taken da ke cewa 'ilmi mai inganci domin ci gaba mai dorewa" a dandalin baje kolin, an samar da rumfuna 80, wadanda aka shirya domin kawo ziyara ta dalibai da kuma shugabanni masu fada a ji a bangaren ilmi. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China