Mr. Ban ya kuma bayyana cewa, kamata ya yi gamayyar kasa da kasa su ci gaba da kokari wajen ganin an tsawaita wa'adin dakatar da musayar wuta a yankin.
Cikin sanarwar tasa, Mr. Ban ya kuma sake yin kira ga bangarorin da rikicin yankin na Gaza ya shafa, da su kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta jin kai ta mako guda, domin fara aiwatar da shirin lumana na shimfida zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Kaza lika babban magatakardan MDD ya jaddada cewa, ya kamata a janye shingen da aka sanyawa yankin na Gaza, a kuma cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin Falesdinu da Isra'ila.
Da safiyar ranar Asabar ne dai kungiyar Hamas da Isra'ila, suka kulla wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta sa'o'i 12, watau tun karfe 8 na safe zuwa 8 na daren wannan rana.
Hukumar kiwon lafiya a Falesdinu dai ta gaskata cewa, tun bayan da sojojin Isra'ila suka fara kaddamar da hare-hare kan yankunan al'ummar Falasdinawa, bisa abin da suka kira kiyaye tsaron iyakar kasarsu, an hallaka Falasdinawa 1030, yayin da sama da 6000 suka jikkata, wadanda kuma galibinsu fararen hula ne.
A bangaren Isra'ila kuwa, mahukunta sun ce sojojin kasar 35 suka hallaka, yayin da kuma sama da 1000 suka jikkata. (Maryam)