Kwamitin ya kuma tsai da kudurin kafa wani kwamitin gudanar da bincike mai 'yanci don binciko dukkan aikace-aikacen keta dokokin jin kai da na hakkin dan Adam na kasa da kasa da aka aikata a wadannan yankunan.
Kasashe mambobin kwamitin kula da harkokin hakkin dan Adam na MDD guda 47 sun kada kuri'u kan kudurin, yayin da kasar Amurka ita kadai ta jefa nuna rashin amincewa da wannan kuduri.
Yayin taron, zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin MDD da ke Geneva, kuma wakilin kungiyoyin kasa da kasa da ke kasar Switzerland Wu Hailong ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna bacin ranta matuka game da hare-haren da aka kai kan fararen hula da ke wadannan yankuna. Ya kuma jaddada cewa, Sin ta bukaci bangarorin da abin ya shafa da su dauki matakan da za su tabbatar da samar wa Falesdinawa 'yancin dan adam ta fuskokin zaman rayuwa, da samun ci gaba, da kuma bin addini da al'adu da dai sauransu. Sin na ganin cewa, abin da ya kamata a gaggauta aiwatarwa yanzu shi ne a dakatar da musayar wuta a tsakanin Falesdinu a Isra'ila ba tare da bata lokaci ba. (Maryam)