A cikin wata sanarwa zuwa ga 'yan jarida, kwamitin na kasashe mambobi 15 ya yi kiran gwamnatin Sudan ta Kudu data gurfanar da dukkan mutanen dake da hannu kan wadannan tashe tashen hankali gaban kotu.
Sanarwar ta kwamitin sulhun ta yi Allah wadai da hare haren da wasu kungiyoyi dauke da makamai suka kai kan fararen hula da kuma tawagar MDD (MINUSS) dake Bor hedkwatar jihar Jonglei dake Sudan ta Kudu a ranar 17 ga watan Afrilu.
Mambobin kwamitin sun nuna takaici game da wadannan hare hare kan fararen hula da sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD da lamarin ya kasance wani babban laifin yaki.
A cewar kafofin watsa labarai, wasu mutane dauke da makamai sun kai hari kan sansanin MDD, inda mutane dubu biyar suke samun wurin mafaka, inda suka kashe mutane 20 da jikkata wasu 70. (Maman Ada)