Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Madan Hua Chunying wadda ta bayyana hakan a ranar jumma'an nan lokacin taron manema labarai tace kasar na fatan ganin yunkurin daga dukkan bangarorin da hakan ya shafa wanda zai taimaka wajen ragen zaman zullumi a kasar Sudan ta Kudu.
Bangarorin masu gaba da juna a Sudan ta Kudu dukkan su sun rattaba hannu akan wata yarjejeniya a ranar 9 ga watan nan da muke ciki wanda a ciki aka amince zasu dakatar da bude wuta sannan a kafa gwamnatin rikon kwarya domin shirin babban zabe a cikin shekara daya. (Fatimah Jibril)