Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bayyana hakan a yau Laraba 23 ga wata a lokacin taron manema labarai a nan Birnin Beijing, dangane da bayanan dake nuna cewa a yankin da hargitsin ya auku an gano gawawwakin fararen hula da dama.
A dangane da hakan, Qing Gang ya ce Sin na kira ga bangarorin da abin ya shafa na kasar Sudan ta Kudu da su ciyar da shawarwarin siyasa dake tsakaninsu gaba, don warware matsalolin da kasar ke fuskanta yadda za a iya shimfida zaman lafiyar kasa cikin sauri, tare da ciyar da harkokin bunkasa kasa gaba. (Maryam)