'Yan sandan kasar Nijeriya sun sheda a ran 28 ga wata cewa, an saki wani dan Birtaniya da aka yi garkuwa da shi kwanaki biyar da suka gabata.
Kakakin hukumar 'yan sanda ya bayyana cewa, 'yan bingida dadi sun dauki wannan dan Birtaniya cikin wata mota kuma sun kai shi wata unguwar gidaje don sake shi, amma bai yi bayani filla-filla ba. Kakakin ya ce, yin garkuwa da baki babban laifi ne, shi ya sa 'yan sanda sun riga sun kara tsananta matakan tsaro da kuma yin bincike.
An ce, an yi garkuwa da wannan mutum ne a cikin gidansa dake tsibirin Victoria a Lagos domin neman kudin fansa daga kamfanin man fetur da yake aiki. (Amina)