140417murtala.m4a
|
Kakakin ma'aikatar tsaro ta Najeriya Chris Olukolade, ya bayar da wata sanarwa a daren ranar Laraba a Abuja, inda ya ce an yi nasarar kubutar da 'yan mata 107 daga 129 da aka sace a garin Chibok dake jihar Borno, inda kawo wannan lokaci 8 suka rage a hannun 'yan bindiga.
Olukolade ya kuma bayyana cewa, sojojin Najeriya sun kama daya daga cikin 'yan bindigar da suka yi garkuwa da 'yan matan.
Tun dai a ranar Laraba, gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya tabbatarwa 'yan jarida cewa, akwai 'yan mata 14 wadanda suka tsira daga hannun 'yan bindiga bayan da aka yi garkuwa da su.
A halin yanzu sojoji na ci gaba da kokarinsu na gano wadannan 'yan mata 8.
Majalisar Dinkin Duniya, da kungiyar tarayyar Turai wato EU, da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, gami da sauran wasu kungiyoyin kasa da kasa, sun yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kaiwa daliban makarantar ta Chibok, da garkuwar da 'yan bindigar suka yi da 'yan matan 129 a jihar ta Borno, tare da bayyana bukatar sakin daliban ba tare da bata lokaci ba.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.