Shugaban hukumar 'yan sandan birnin Ikko Umar Manko ya bayyana cewa, bayan an kwato shi daga hannun masu yin garkuwa da shi, Lee ya koma gida domin duba lafiyarsa. Har ila yau Manko ya ce, an gano wasu makamai a wurin masu yin garkuwa. Amma bai yi cikakken bayani kan yadda aka gudanar da aikin ceto ba.
Yayin da Dickson Lee ke dawowa daga filin jirgin saman birnin Ikko ran 16 ga wata ne dai, wasu dakaru dauke da makamai da ba a san ko suwaye ba suka yi garkuwa da shi, suka kuma raunata direbansa. (Maryam)