Rahotanni daga rundunar 'yan sandan Jihar Anambra dake kudancin tarayyar Najeriya, na bayyana cewa an hallaka wasu mutane 7 da ake zaton masu garkuwa da mutane ne a Aguleri, dake karamar hukumar Anambra ta Gabas.
Kakakin rundunar dake jihar Emeka Chukwuemeka, ya bayyanawa manema labaru cewa, an kame wasu karin mutane 2 da ake zarginsu da kasancewa cikin wannan rukuni na bata-gari, dai dai lokacin da suke kokarin karbar wasu kudin fansa da suka kai naira miliyan 5 a ranar Juma'ar data gabata.
Yayin farmakin da jami'an tsaron suka kai maboyar bata-garin da taimakon wadanda aka kame din, sun samu nasarar ceto wasu mutane da aka tsare, ciki hadda wani dan kwangila dan asalin kasar Lebanon, wanda aka kame tun ranar 7 ga watan nan na Mayu. (Saminu)