in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kunar bakin waken da suka kai hari a yankin Agadez sun yi garkuwa da wasu sojojin Niger
2013-05-24 19:49:29 cri
Yanzu haka sojojin Niger din nan da aka yi garkuwa da su,suna tsare ne a wani gida a kusa da barikin soja na Agadez da ke arewacin kasar.

Ministan cikin gida na Jamhuriyar Niger Abdou Labo ya bayyana cewa, dan kunar bakin waken ya kulle kansa a cikin gidan da ke kusa da barikin sojan na Agadez tare da matasan sojojin da aka yi garkuwa da su.

Wata majiyar soja ta bayyana cewa,an yi wa gidan kawanya kuma an dauki matakan da suka dace don ganin an kama dan kunar bakin waken tare da kwato sojojin da ake garkuwar da su.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China