Rahotanni daga jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar Najeriya na cewa, sama da dalibai 'yan mata 100 ne 'yan kungiyar nan ta Boko Haram suka yi awon gaba da su, daga kwalejin 'yan mata dake garin Chibok.
A cewar jami'in rundunar 'yan sandan yankin Lawan Tanko, tuni aka fara bincike tare da daukar matakan kubutar da daliban.
Mazauna yankin da wannan lamari ya auku sun ce, maharan dauke da bindigogi sun yi dirar mikiya a kwalejin 'yan matan ne, suka kuma tisa keyar dalibai 105 daga dakunan kwanansu.
Kaza lika wani mazaunin garin na Chibok ya bayyanawa manema labarai cewa, 'yan bindigar sun hallaka soja daya, tare da raunata wasu magidanta, da suka yi kokarin hana aukuwar harin. Ya ce, ba a kashe kowa cikin daliban ba, sai dai firgita su da 'yan bindigar suka yi.
Watanni biyu da suka gabata ma dai sai da 'yan bindiga suka hallaka yara 'yan makaranta 40, yayin wani hari da suka kaddamar a garin Buni Yadi na jihar Yobe.
Jihohin Borno da Yobe da Adamawa dai na karkashin dokar ta baci kusan watanni 12 da suka gabata, sakamakon yawan aukuwar hare-haren da 'yan Boko Haram ke kaddamawa a sassan jihohin daban daban. (Saminu)