Mahara sun yi awon gaba da wasu Sinawa injiniyoyi su 2, dake aiki da wani kamfanin hakar danyan mai a jihar yammacin Kordofan dake kasar Sudan.
Wata majiya a ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Khartoum ta ce, an sace Sinawan ne a ranar Juma'ar da ta gabata. Majiyar ta kuma ce, tuni ofishin jikadancin ya mika bukatar gaggauta daukar matakan sako su, ga hukumomin tsaron kasar da lamarin ya shafa.
Wasu kafofin watsa labarun kasar ta Sudan sun bayyana cewa, wasu maharan kungiyar JEM ne suka yi dirar mikiya mahakar danyan man dake garin Balila a jihar yammacin Kordofan, inda nan take suka tisa keyar ma'aikatan kamfanin GNPOC dake aiki a wurin su uku, da suka hada da Sinawa biyu da wani dan Sudan daya. (Saminu)