A lokacin ganawar, Mr Zhang ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Nigeria ta zama abin koyi ga sauran kasashe saboda ganin ta shafi bangarori daban-daban bisa manyan tsare-tsare, ban da haka an samu ci gaba mai yakini a fannoni daban-daban. Kwanan baya kuma, Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya cimma nasarar a ziyararsa da ya kai Nigeria, inda bangarorin biyu sun daddale yarjeniyoyi da dama kan kara zuba jari da yin hadin kai, matakin da ya samar da wata makoma mai haske wajen zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu.
A nasa bangare, Mr Mark ya ce, Sin sahihiyar abokiyar Nigeria ce, gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasashen Afrika taimako a fannin raya tattalin arziki da al'ummominsu ciki hadda Nigeria, abin da zai kawo amfani sosai a cikin dogon lokaci. (Amina)