Kasar Ghana za ta shirya wani dandalin tattalin arziki na kasa a cikin makon karshe na watan Mayu, in ji mataimakin shugaban kasa Kwesi Bekoe Amissah-Arthur a ranar Talata a birnin Accra.
Ministan kudin Ghana ya gabatarwa gwamnati da wani kundin da yanzu haka aka gyara domin wannan dandalin tattalin arziki na kasar da za a shirya, a cewar mista Amissah-Arthur.
Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan sanarwa a lokacin jerin tattaunawar siyasar shekara shekara ta shekarar 2014 tsakanin Ghana da kungiyar tarayyar Turai EU, inda suka mai da hankali kan hanyoyin karfafa dangantaka tsakanin Ghana da EU.
Haka zalika yayin dandalin, za a yi kokarin samar da shawarwari kan matakan da za'a dauka domin cimma maradun kasafin kasa na shekarar 2014, in ji mista Amissah-Arthur tare da bayyana cewa, taron zai gudana a ranar 19 zuwa 22 ga watan Mayu. (Maman Ada)