Babban bankin cigaban Afrika (BAD) ya amince da kafa wani sabon asusu kan sauyin yanayi da zai taimaka wajen gaggauta sauyin nahiyar Afrika zuwa wani tattalin arziki mai tsafta.
Asusun Afrika kan sauyin yanayi (FACC), wani asusun aiki ne na kasa da kasa da zai taimakawa kasashen Afrika bisa hanyarsu ta rungumar cigaban dake zuwa daidai muhalli da rage hayakin dake gurbata muhalli.
Akwai babbar dama ga bankin domin daidaita da zuba kudi wajen kare muhalli zuwa Afrika, in ji darektan sashen makamashi, muhalli da sauyin yanayi na bankin BAD mista Alex Rugamba a cikin wata sanarwa da aka bayar a ranar Laraba a birnin Nairobi.
Mista Rugamba ya bayyana cewa, Afrika nahiya ce wadda ta fi fuskantar sakamakon canjin yanayi, amma kuma nahiyar tana samun karamin kaso na kudaden da suka shafi matsalar sauyin yanayi idan aka kwatanta da sauran nahiyoyin duniya.
Na yi imanin cewa, nauyin bankin BAD ne na taimakawa kasashen Afrika wajen samun wadannan kudaden kasa da kasa game sauyin yanayi domin tallafawa sauyin nahiyar zuwa wani cigaban tattalin arziki maras gurbata mullahi, in ji wannan jami'i.
Bankin BAD zai karbi da kula da asusun FACC da aka kafa, tare da taimakon kudin Euro miliyan 4,725 daga kasar Jamus bisa wa'adin farko na shekaru uku. (Maman Ada)